Dan takarar jam’iyar PDP, Ademola Adelekw yayi nasarar lashe zaben gwamnan jighar Osun.
Inda ya kwace mulkin jihar daga hannun Gboyega dan takarar APC dake son komawa ofishin nasa.
Ademola Adeleke yayi nasarar lashe zaben a kananun hukumomi 17 ne yayin da APC tayi nasara a kananun hukuma 13 cikin 30 na jihar.
Kuna akwai tazarar kuru’u a tsakaninsu domin Adleke ya samu 402,979 ne yayin da shi kuma Oyetola ya samu 375,077.