Kungiyar kare hakkin bil’adama ta HIRIWA ta bayyana cewa sakon Kirismetin da shugaba muhammdu Buhari ya turawa Kiristoci bashi da ma’ana da alkibla.
Shugaban kungiyar ta HIRIWA, Emmanuel Onwubiko ne ya bayyana cewa sakon Kirismetin na Buhari bashi da alkibla,
Domin gwamnatin shugaba Muhammdu Buhari ta saka al’ummar Najeriya guda miliyan 130 cikin bakin talauci.
A sakon shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta habbaka harkar noma da tsaro da magance talauci, amma HURIWA tace ba haka bane domin Naneriya kara tabarbarewa tayi a mulkin Buhari.