Ga Sakon soyayya na safe masu ratsa zuciya.
Na kwanta da tunaninki na tashi da shi, kece ta farko data fara saka min irin wannan yanayi.
Nayi mafarkin na mallakeki, Allah ya cika kin burina.
Ga sakona, ina son ya zama abu na farko da zai saki murmushi ayau.
Fararen idanunki, murmushinki me sanya nutsuwa, annurin dake fuskarki, fatarki me sheki kamar gwal, su nake son in fara aba dasu idan na tashi da safe.
Idan na tashi da safe wayata ba caji, ba data, ke nake tunawa inta nishadi.
Ashe har a baccima ana soyayya, jiya bayan na kwanta sai naji an kama hannuna ance zo muje yawo, dana bude ido sai naga kece.
Ina fatan kin tashi qalau, ki yi farin ciki dan tabbas akwai wanda ke sonki si na hakika.
Badan baba da mama kar suke na haukace ba, dana rika zuwa kullun muna karyawa tare.
Safiyata bata cika sai naji muryarki.
Idan na tashi da safe sai inta juyi akan gado in kasa tashi, inata tunaninki.