fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Sakonnin soyayya masu ratsa zuciya

Ga Sakonnin soyayya masu ratsa zuciya wanda zasu sa ka kara shiga zuciyar masoyiyarka.

 

Kina raina koda yaushe, Tunaninki ya zama abinci na da ruwan shana wanda dana yi shi nake samun nutsuwa.

 

Nutsuwata na tattare da farin cikinki, idan naga mumushinki sai inji raina yayi fari.

 

Kallon fuskarki na sani nishadi irin wanda ake ji in ana kallon sabbin kudi.

 

Naman kaza nafi so, amma idan ina tare dake sai inji kawai na koshi dashi.

 

Idan kika ci abinda nake so, sai inji kamar ni naci.

 

Dukiyata takice, ki yi yanda kike so da ita.

 

Idan ina da ke, bana bukatar abokai ko wani abin debe kewa, kin isheni nishadin rayuwa.

 

Wutar lantarki itace karshen sokin, amma idan ina tare dake ina jin shokin din da yafi na wutar lantarki karfi.

 

Kece ranata ta, kina shigowa rayuwata ta yi haske.

 

Ni nagama mun fara kama da juna saboda tsabar son da mukewa junanmu.

 

Badan ana bukatar kudi a rayuwa ba, in zauna ina kallonki ya fi min zuwa kasuwa.

 

Kwalliyarki na rikirkitani.

 

Kullun fuskarki sheki take kamar hasken rana.

 

Ina sonki fiye da yanda nake son kaina.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *