fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Sakonnin soyayya na dare

Ga Sakonnin soyayya na dare masu kara dankon soyayya.

 

Zan kwanta da tunaninki, watakila in yi mafarkin mun yi aure.

 

Gadona yamin kadan, Tunaninki ke sakamin nutsuwa inji ya wadaceni.

 

Ina miki fatan ki tashi kamar jaririya an gafarta miki zunubanki.

 

Dare mahutar bawa, hutuna in kasance tare dake.

 

Abincin darena yana min lami idan ban kiraki naji muryarki ba.

 

Ga farin wata yayi haske, taurari sun kawata sararin samaniya, ina bukatarki kusa dani mu kallesu tare.

 

Bana bukatar kallon duk wani fim, ko waka, ko kasancewa tare da wani a wannan lokaci, kece kawai nake da bukata.

 

Bayan dana bar gidanku, tunaninki na yi ta yi, har na wuce gidan mu ban sani ba.

 

An kawo min abincin dare amma tunaninki yasa har yayi sanyi ban ci ba.

 

Ba dan dole in baiwa jikina hakkinsa na bacci ba, sannan kema in kare mutuncin ki ba, da ban dawo gida daga wajenki ba.

 

Zan Kwanta cikin farin ciki sanin cewa ina da masoyiya ta gaskiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *