fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Sama da mutane 200 ne ‘yan Bindiga suka kashe a Zamfara a sabon harin da suka kai

A sabon harin da ‘yan Bindiga suka kai jihar Zamfara tsakanin ranar Talata, sun kashe mutane akalla 200.

 

Lamarin ya farune a rafin Danya da Barayar Zaki, Rafin Gero da Kurfa.

 

Rabotan yace ‘yan Bindigar na tserewa ne daga jihar Zamfara yayin da suka kai hare-haren a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.

 

Wanda suka tsira daga harin sun ce an kashe mutane akalla 200 sannan kuma an kona gidaje.

 

Wanishaida me suna Muhammad Kurfa yace ‘yan Bijilante sun so tare ‘yan Bindigar dake da yawa inda suka dara musayar wuta, yace ‘yan Bindigar na tare da shanu akalla dubu 3.

Karanta wannan  Ka fadawa mabiyanka su daina min kazafi, Tinubu ya fadawa Peter Obi

 

Hakanam Kamfanin AP yace wata majiya tace sun kashe duk wani matashi da ya kai shekaru 20.

 

Yayin da aka binne wasu, wasu kuwa ana kan  neman inda suke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.