Shugaban kungiyar masu sa’ar ababen hawa na A Daidaita Sahu da kuma babur wanda aka fi sani da Okada, Usman Gwoza ya kalubalanci hana tuka babura da shugaba Buhari yake shirin yi.
Gwoza ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na NTA a ranar litinin, inda yace hakan bai dace sam don ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba.
Ya kara da cewa masu tuka babura a fafin Najeriya sun fi karfin miliyan 20 amma guda miliyan 14 ne suka yi rigista, kuma idan aka hanasu wannan aikin duka zasi fada cikin bakin talauci.
Domin da wannan sana’ar ne suke ciyar da iyalansu har ma su samu abin kashwa, saboda haka ya kamata gwamnagin tarayya ta waiwayi wannan lamarin.