Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta bayyana cewa sama da shaguna 100 sun babbake a gobarar data auku a kasuwar Bodija dake babban birnin jihar Oyo wato Ibadan.
Hukumar ta kara da cewa sama da shaguna 350 gobarar ta shafa amma a cikin sama da 100 suka babbake bakidaya a ranar litinin.
Kuma anyi asarar kayayyakin miliyoyin naira a kasuwar sakamakon gobarar wacce ba a san dalilin daya kawo ta ba.
Amma masu hannu da tsaki a kasuwar da hukumar bada agajin gaggawar sun gagauta zuwa kasuwar sun kawo masu dauki.