fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Sama da watanni 3 bayan da Majalisa ta amince da Nadin Ambasadoji har yanzu Shugaba Buhari bai basu aiki ba

Sama da kwanaki 96 da Majalisar Tarayya ta amincewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan sunayen Ambasadoji 42 har yanzu gwamnati bata sanar dasu a inda zasu yi aiki ba.

 

Hakanam basu ma san ranar da zasu fara aikin ba, kamar yanda Hutudole ya samo muku daga Punch. Hakanan kuma a watan Yuli na shekarar 2020, Shugaban kasar ya kuma samu amincewar majalisar kan karin wasu ambasadojin 39 wanda suma har yanzu ba’a basu aikin da zasu yi ba.

Wani Ambasada da baiso a ambaci sunansa ba ya bayyanawa majiyar tamu cewa rashin kudi da rashin tsari ne na gwamnati yasa har yanzu ba’a baiwa sabbin ambasadojin aiki ba.

 

Yace yasan gwamnati zata iya fakewa da zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 kan rashin baiwa ambasadojin aiki amma idan aka tuna haka ta faru da ambasadojin da shugaba Buhari ya nada a shekarar 2016,sai a shekarar 2017 sannan aka basu wajan aiki. Yace saida suka kwashe watanni 6 bayan nadinsu sannan suka fara aiki.

Karanta wannan  Sakamakon jarabawata ta WAEC ta bata amma tayi matukar kyau don ni ne dalibi na biyu dayafi kokari a shekarar, cewar mataimakin Atiku, Okowa

 

Yace abinda ake yi shine idan aka aikawa kasa da sunan ambasada sai ta amince dashi tukuna ya fara aiki yace idan ga amince dashi to za’a bashi takarda a aikashi kasar da zai je, yace abu ne dake daukar lokaci me tsawo amma dai ya danganta da irin alakar dake tsakanin kasashen 2.

 

Yace amma matsalar da gqamnatin ke fuskanta shine tana son yin aikin tura ambasadojin a lokaci 1 ne maimakon a yisu daya bayan daya. Yace wani karin lamari shine yawancin Ambasadojin manyan ‘yan siyasa ne irin su gwamnoni suka tura sunayensu dan hakane ma suke ta bin kafar a turasu manyan kasashen Duniya irin su Amurka da Ingila.

 

Da majiyar ta tuntubi ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya, tace umarnin shugaban kasa take jira kamin ta fara aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.