fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Samar da ‘yansandan jihohi ba shine mafita ba>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi watsi da kiran kafa ‘yansandan jihohi a Najeriya inda yace bashine mafita ba.

 

Gwamnonin jihohi da dama ne suka nemi a kafa ‘yansandan jihohi bisa hasashen cewa hakan zai taimaka wajan rage matsalar tsaro.

 

Shugaba Buhari yace akwai yiyuwar Gwamnonin su rika amfani da ‘yansandan jihohin ta hanyar da bata dace ba idan aka kafasu.

 

Ya bayyana hakane a Channels TV yayin wata hira da suka yi dashi.

 

Shugaba Buhari yace, sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawar da zasu taka wajan magance matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published.