fbpx
Monday, December 5
Shadow

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Assalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu, Masu bibiyar shafin hutudole.com da kuma masu shafuka da mukayi alkawari dasu zasu rika wallafa labaranmu, wannan sanarwar takuce. Wani bincike da shafin hutudole.com ya gudanar, ya gano cewa wasu manya da kananan shafukan labarai na daukar labaranmu suna wallafawa a shafukansu a matsayin nasu ba tare da bayar da hakkin mallakaba.

Wannnan yasa muka dauki matakin rage wannan abu dake faruwa, saboda be kamataba. Idan za’a lura, a labaran yau da muka wallafa mun rubuta haruffan (H.T.D.L) a jikin wasu hotuna wanda hakan yana nufin hutudole ne a takaice. To haka zamu cigaba da rubuta irin wadannan harufa in Allah ya yarda a jikin hoton duk wani labari da mune muka wallafashi, ba daukoshi mukayi daga wani shafiba, kamar yanda kuka sani idan muka dauko labari daga wani shafi, mukan bayar da hakkin mallaka, mu fadi daga inda muka daukoshi, saidai wataran akwai ajizanci irin na dan Adam da kuma mantuwa.
A labarin gamagari, musamman na siyasa, koda mune muka wallafashi bazamu rubuta wadannan harufaba, amma a sauran labarai zamu rika rubutawa dan a rika banbancewa. Hakan bawai zai yi maganin wannan matsalar bane gaba daya, amma zai rageta zuwa wani mataki.
Rubuta wadannan haruffa a jikin hotuna bawai yana nufin shafin hutudole ne keda hakkin mallakar gabadayan hotunan ba, a’a hakkin mallakar labarine kawai, kuma hakan zai cigaba zuwa wani lokacine da idan Allah ya kaimu zamu daina yin hakan.
Mun san cewa yin rubutu a jikin hoto yana ragewa hoton kyau da sauran wasu abubuwa, shiyawa muke baiwa masu karatu da masu shafuka da mukayi alkawari dasu zasu rika wallafa labaranmu hakuri, nadan wani lokacine, in Allah ya yarda zai wuce.
Mun gode.
Hutudole.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Kalli Bidiyo: Shi Ma Fa Aminu Ya Ci Kudin Talakawa Domin An Dana Shi A Jirgin Gwamnati

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *