fbpx
Monday, June 27
Shadow

Sanata Aliero da jiga-jigan jam’iyyar APC a Kebbi sama da 30 sun koma PDP

Tsohon gwamna, sanata Adamu Aliero da ya bar jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP ya ce rashin adalci da aka nuna wajen zaɓen fitar da gwani a Kebbi na daga cikin dalilansa na sauya sheka.

Aliero wanda ya taba zama gwamna a Kebbi har sau biyu da kuma tsohon minista a Abuja ya shaida hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yana jadada rashin jindadinsa kan yada ake tafiyar da harkan jam’iyyar APC a Kebbi.

Tsohon gwamnan da kuma ya taba sanata har sau uku ya ce bai ɗau wannan hukunci ba, sai da ya yi tuntuɓa da magoya-baya da masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci komawa jam’iyyar da za ta yi musu adalci wajen sake gina kasa.

Karanta wannan  Har yanzu ina cigaba da neman abokin takara na, cewar Bola Tinubu

Sanata Adamu Aliero ya sauye sheƙa tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar a Kebbi sama da 30, da suka hada da tsohon gwamnan Kebbi, Sa’idu Usman Nasamu Dakingari da Sanata Yahaya Abdullahi da kuma tsohon mataimakin shugaban kwastam, Muhammad Mera.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.