fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Sanata Bukola Saraki yace Najeriya ta talauce, an sace Tirliyan 2 a gwamnatin Buhari

Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki wanda kuma yana cikin masu neman takarar shugaban kasa yace Najeriya ta talauce.

 

Yace kamfanin NNPC na kasa ya kwashe watanni da yawa bai kawo gudummawar kudi ba a asusun gwamnati.

 

Taohon gwamnan Kwaran ya bayyana cewa a kullun ana sace danyen man Najeriya da ya kai lita miliyan 70 wanda kuma yace a duk shekara Najeriya na asarar Dala Biliyan $2 wajan biyan kudin tallafin mai na karya.

 

A kwanakin baya dai dan kasuwa Tony Elumelu ya bayyana cewa, kusan kaso 90 cikin 100 na danyen man Najeriya saceshi ake, saidai karamin ministan man fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa ba haka zancen yake ba, abinda Tony Elumelu ya sani ne yake fada.

Karanta wannan  Ka fadawa mabiyanka su daina min kazafi, Tinubu ya fadawa Peter Obi

 

Sylva ya tabbatar da cewa lallai ana satar danyen man a kullun da ya kai akalla ganga 200,000 wanda kusan Naira Biliyan 8 kenan.

 

A nashi bangaren, Saraki yace ba zai zama shugaban kasa ace mafi yawan danyen man Najeriya saceshi ake ba.

 

Saraki yace lokacin yana kakakin majalisa ya bayyana cewa kudin tallafin man fetur da ake bayarwa na karyane.

 

Yace hakan yasa EFCC ta fara bincikensa amma duk da haka bai hakura ba.

 

Saraki yace Tirliyan 2 ake asara dalilin badakalar danyen mai wanda yace idan ya zama shugaban kasa zai dakatar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.