fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Sanata Ndume ya amince ya tsayawa Abdulrashid Maina a bada belinshi

Tsohon shugabab Hukumar gyaran Fansho ta kasa,Abdulrashid Maina ya bayyana cewa ya samo Sanata Ali Ndume a matsayin wanda zai tsaya mai a bada belinshi.

 

Maina ya bayyana hakane a zaman da kotu ta yi yau, Talata na ci gaba da sauraren kararsa. Ya bayyana hakane ta bakin lauyansa, Joe-Kyari Gadzama(SAN). Ndume dai bai halarci zaman kotun ba amma Maina ya bada tabbacin cewa ya amince ya tsayamai.

EFCC dai na tuhumar Maina bisa almundahanar makudan kudi. A baya kotun ta bada belinshi akan Biliyan 1 da kuma sanatoci 2 da zasu tsaya mai wanda dole sai suna da gida a birnin Abuja na akalla Naira Miliyan 500.

 

Maina bayan ya kasa cika wannan sharudan Beli ya roki kotu ta sassauta mai inda ta yadda tace yanzu ya samo sanata 1 da Miliyan 500.

Karanta wannan  An shawarci Peter Obi ya nemi naira biliyan hamsin idan har yanaso ya kayar da Tinubu a zaben 2023

 

Wannan ma ya kasa cikashi inda ya kara neman a rage mai, abinda kotun ta kiya. A zaman kotun na yau ya janye neman sake sassauta mai sharudan Belin inda yace Sanata Ndume ya tsaya mai. Lauyanshi yace yana bukatar kulawar likita sosai.

 

Amma lauyan EFCC, Farouk Abdallah ya soki wannan bukata.

 

Mai shari’a Abang ya saka ranar Yuni 29 ga watan dan yanke hukunci akan lamarin Belin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.