fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Sanata Shehu Sani ya bayyana hanya daya wadda ta hakane kawai dan kudu zai zama shugaban kasa a 2023

Sanata Shehu Sani daga Kaduna ya bayyana hanya daya da zata iya kai ga dan kudu ya zama shugaban kasa a 2023.

 

Anata ta cece-kuce kan wanda zai gaji shugaban kasa,Muhammadu Buhari kuma daga wane yanki zai fito.

 

Saidai Sanata Sani a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter ya bayyana cewa, idan manyan jam’iyyun Najeriya sun tsayar da ‘yan kudu ne kadai za’a iya samun shugaban kasa daga kudu.

 

Shima dai Sanata Shehu sani ya fito takarar gwamnan jihar Kaduna inda za’a fafata dashi a zaben fidda gwanin dan takara.

Karanta wannan  Sakamakon jarabawata ta WAEC ta bata amma tayi matukar kyau don ni ne dalibi na biyu dayafi kokari a shekarar, cewar mataimakin Atiku, Okowa

 

Kuma tuni yayi alkawarin cewa, idan ya zama gwamnan, diyarsa makarantar gwamnati zata koma da karatu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.