Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa masu neman shugabancin kasar nan a jam’iyyar APC mai mulki ke bayyana hanyoyin magance matsalolin Najeriya da dama idan aka zabe shi, amma ba su ba shugaban Najeriyar na yanzu haka mafita ba.
Da yake magana a shafin Twitter a yammacin Lahadi, 17 ga Afrilu, Sanata Sani ya ce;
“Dukkan masu neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyya mai mulki suna da tarin hanyoyi na warware matsalolin kasar nan. Me ya sa suka boye wannan baiwar da suke da a halin yanzu da ake bukatar ta?”