Friday, May 29
Shadow

Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya taya daukacin al’ummar musulmai barka da sallah

Kasancewar watan Azumi na shekarar 2020 ya kammala a ranar 23 ga watan Mayu, al’umma daban daban na shirin fara bikin karamar Sallah wanda za’a fara shi a gobe lahadi.

 

Sanatan kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Shekarau ya aike da sakon taya daukacin musulmai barka da sallah wanda zai gudana a ranar lahadi.

Shekarau ya bayyana cewa “duk da cewa muna a wani yanayi da muka samu kan mu a ciki a sakamakon cutar Coronavirus wanda galibi musulmai baza su iya yin bukukuwa ba a sakamakon cutar Covid19.

Wajubi ne a gare mu damu taimakawa gwamnati domin ya kar cutar corona wacce ta taba rayuwar mutane tare da gurgunta tattalin arzikin kasa.

 

Sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa wadda ya sanyawa hannu a ranar Asabar.

Haka zalika ya yaba da aikin da kwamitin yaki da cutar coronairus ke yi, tare da yin addu’a ga daukancin wadanda suka rasa ransu a wannan yanayi.

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *