fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Sanatan APC ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta tsayar da Musulmai a matsayin ‘yan takararta ne don ta kawar da hankulan talakawa daga kurakuran da Buhari ya tafka

Sanatan APC dake wakiltar Arewacin jihar Adamawa, Elisha Abbo ya bayyana dalilin dayasa jam’iyyar su ta APC ta tsayar da Musulmai a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa.

Inda yace tayi hakan ne domin takawar da hankulan mutane sun mance da kurakuran da shugaban Buhari ya tafka a mulkinsa.

Kuma sanatan ya kara da cewa majalissar dattawa ba zata iya kare kanta akan lunkume naira triliyan hudu datayi ba na kudin man fetur.

Kuma yace shi dan APC ne amma vaya ba mutane shawara su zabi Tinubu a zabe mai zuwa domin ya fice daga kungiyar dake yiwa Tinubu yakin neman zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.