Mafi yawancin sanatocin Najeriya sun goyi bayan shirin tsige shugban kasa Muhammdu Buhari akan mulki kan matsalar tsaron da kasar ke fama dashi.
Dan majalissar dattawa dake wajiltar arewacin jihar Bauchi, sanata Adamu Bulkachuwa ne ya bayyana hakan ranar litinin yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels.
Sanatan APC din ya kara da cewa sunyi iya bakin kokarinsu don su taimakawa gwamnatin tarayya a magance matsalar tsaro amma a kullun abin kara tabarbarewa yake yi.
Saboda haka a karshe shawarar da suka yanke kawai itace a tsige shugaban kasar domin a samu saukin matsalar tsaron a kasar.