fbpx
Monday, August 15
Shadow

Sanatan jihar Adamawa ya dawo daga rakiyar Tinubu saboda ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa

Sanatan dake wakiltar arewacin jihar Adamawa, Elisha Ishaku Abbo ya bayyana cewa ya fita a cikin kungiyar dake yiwa Tinubu yakin neman zabe.

Sanatan ya fita a tawagar ne saboda Tinubu ya zabi Musulmi dan uwanshi a matsayin abokin takararsa na shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Inda yace abinda yayi bai kamata ba domin zai iya raba kan ‘yan Najeriya kuma dama yaso yayi hakan a shekarar 2015 amma Buhari yaki amince masa.

A ranar lahadi ne Tinubu ya bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.