fbpx
Friday, August 12
Shadow

Sanatoci sun fice daga majalissar dattawa ana tsaka zama kan batun matsalar tsaro da kuma tsige shugaba Buhari

Sanatocin jam’iyyun daba na APC ba sun fice daga majalissar dattawa ana tsaka da zama kan matsalar tsaro da kuma batun tsige shugaba Buhari.

A yau ranar laraba ne wannan abin ya faru kuma sun fusata sun fice ne bayan shugaban sanatoci Ahmad Lawal yaki goyon bayan a tsige Buhari.

Karamin shugaban Sanatoci Aduda ne ya jagorancesu suka fice kuma yace suna nan akan bakarsu ta tsige shugaban kasar.

Inda yace makonni shida kacal suka bashi ya magance matsalar ko kuma su tsige shi domin a kullun harkar tsaro kara tabarbarewa take.

Leave a Reply

Your email address will not be published.