fbpx
Friday, December 2
Shadow

Sanatoci sunyi watsi da kudurin kafa dokar karba karba da zata baiwa kowace kabila damar shugabanci a Najeriya

Majalissar dattawa tayi watsi da kudurin kafa dokar karba karba wadda zata baiwa kowace kabila damar mulkar Najeriya.

Sanatan dake wakiltar kudancin jihar Benue, Abba Moro ne ya nemi a kafa wannan dokar, amma sai dai burin nasa bai cika ba domin abokan aikin nasa sun juyawa shawarar tashi baya.

Inda wasu daga cikinsu suka bayyana cewa kudin tsarin mulki ya baiwa kowa damar tsayawa takarar neman shugabanci saboda haka ba sai an kafa dokar ba.

Inda wasu suka bayyana cewa tsohon shugaban kasa GoodLuck Ebele Jonathan yayi mulki ba tare da an kafa wannan dokar ba.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *