Sarkin Alor dake karamar hukumar Idemili a jihar Anambra, Anthony Okonko yaki barin fada bayan an sauke sa akan mulki.
Watanni biyar kenan da babbar kotun jihar ta tsige shi akan mulkin, wato tun a watan febrairu kenan amma yayi burus yaki barin fada.
Yayin da kuma har al’ummar garin na Alor suka zabi sabon shugabansu wanda suke so ya mulke, Igwe Collins amma Okonko yaki sauka a mulki.
Wanda hakan yasa matasan garin sukace zasu dauki mataki a hannunsu idan har gwamnati batayi wani abu akai ba.