fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya kai ziyarar Karfafa zumunci zuwa Masarautu 4 A Jihar Jigawa

A ranar Litinin mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shirya kai wata ziyarar karfafa zumunci zuwa ga masarautun Gumel,Ringim, Hadeja, da kuma Dutse a jihar Jigawa.

A ranar litinin din dai, Sarkin kano ya fara kai wannan ziyara zuwa ga sarkin Gumel Alh. Ahmad Muhammad Sani II con ziyara ta girmamawa da karfafa zumunci.

Ya kuma kai makamancin irinta zuwa sauran sarakunan da suka hada da sarkin Hadejia Alh. Dakta. Adamu Abubakar Maje CON, da kuma sarkin Ringim Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmud, CON. tare da Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, CFR.

Daga bisani Maimartaba Sarkin kano ya kai ziyara zuwa Gidan Gwmanatin jihar, Inda ya gana da Gwamna Badaru Abubakar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *