fbpx
Thursday, March 4
Shadow

Sau 4 ina daukar ciki yana zubewa tun bayan da uwar Mijina ta Min Baki>>Wata Mata me neman dauki

Wata Baiwar Allah da ta zauna gidan Mijinta babu dadi tana neman taimako dan a kwato mata hakkinta.

 

Ga labarinta kamar haka:

 

Sunana (Hauwa) an boye sunan, nayi aure 16 December 2018.. tun bayan aurena ban San menene farin ciki da kwanciyar hankali ba.uwar Miji na bata Sona ta tsaneni,Ana nan na samu ciki,bayan wata 4 cikin ya zube… tun lokacin mahaifiyar Miji na ta fadi wata kalma tace “wallahi idan har yahaya jini na ne Jamila bazaki goya da a BAYANKI BA” Ana nan dai na sake samun wani cikin bayan wata Tara na haifi yarinya bata zo da Rai ba..bayan nayi kwana 2 na tafi gida wanka..wallahi babu kudin itace,babu kudin nama,babu komai wacce akasan me jego tana bukata..hana rantsuwa ya bani gero mudu 2 da #200..bayan nayi arba,in na koma na samu wani cikin bayan ya tsufa nakuda ta taso da matsala ina bleeding..na tafi gidan mu iyayena suka kaini asibiti bayan an dubani akace c.s za,amin domin yaron ya mutu a ciki…akayi aka ciro yaron komai da kuka sani Wanda akeyi na c.s iyayena suka biya hatta kudin magani..dangin Mijina babu Wanda yazo….maman shi ta dage akan cewa dole se ya sakeni..aka dai dai ta dai aka maidani..bayan na koma na sake samun ciki bayan cikin ya tsufa nakuda ta taso min a gida,inajin ciwo na Kira mijina a waya yace in zauna a gida kar in tafi asibiti…da abun yaki ci yaki cinyewa nace masa asibiti zan tafi..na tashi na tafi asibiti akamin scanning kaka ta ta biya kudin scanning din…na dawo gida..karfe 9:00 na dare naje yin fitsari se naga jini nace wa Miji na Ina bleeding yace Wai in tafi chemist..nace masa ai wannan yafi karfin chemist..muka tashe muka tafi asibiti..aka bani gado a dakin mata bayan an kwantar Dani se naji bleeding din yayi yawa..nacewa doctor ina bleeding kuma ga tsohon ciki,aka turani maternity”wallahi tallahi tun lokacin da suka kaini maternity aka bani gado suka fita batu na gashi jini se zuba yakeyi..idan nace likitoci su temakamin se suce mijina be kawo kayan aiki ba..tun Ina iya magana har bana iya magana…a haka dai har gari ya waye..na samu na Kira mama na na sanar da ita tazo asibitin akace ana bukatar jini leda 3 dangin mama na suka bada 2 Miji na ya bada leda 1..aka samu akamin aikin wallahi ko gama farfadowa banyi ba uwar mijina ta fara bala,I wai ita ta gaji da mutuwar da yarana sukeyi..Wai me yasa Yara suke mutuwa..tayi ta zage zage,Wai idan dai har ta haihu cikin uwarta ta ubanta se mijina ya sakeni…wallahi Ni kam na tsorata kar su kashe Ni…bayan anyi sallama na koma gida…mijina ya zo so 2…kuma ya bani dubu 2 bayan dubu 2 be sake bani ko sisi ba…amma dai shi ya biya kudin aikin..kaf dangin sa babu Wanda yake Sona..Shima yanzu ko a waya baya kirana..kuma yace “he is not interested in me any more” ga kuma kalmar da maman shi tace IDAN HAR INA RAYE Hauwa BAZA KI GOYA DA A BAYANKI BA INDAI HAR YAHAYA JINI NA NE..yanzu abunda ban fahimta ba shine asiri tamin yaran suke mutuwa ko kuma kambun bakan ta ne ya kamami..kar yaron ta ya sakeni inyi wani auren in tafi da bakin bakin da tamin… please a Nemo min hakki na…farko abun be dameni ba kasancewar komai na ALLAH ne Amma su sun nuna sun gaji.

Daga Jihar Naija.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *