fbpx
Friday, August 12
Shadow

Sau 44 ana kaiwa gwamnatin Buhari rahoto cewa za a kai hari gidan kurkukun Kuje, cewar mataimakin kakakin majalissa

Mataimakin kakakin majalissar wakilai, Ahmad Idris Wase ya bayyana cewa an kaiwa gwamnatin Buhari rahotanni sau 44 kafin ‘yan bindiga su kai hari gidan kurkukun Kuje.

Ya bayyana hakan yayi ganawa da manema labarai kan dakatar da hawa babura da gwamnatin Buhari ke shirin yi a fadin kasar nan.

Inda yace babu wani hari da ake kaiwa face an fadawa gwamnati kafin akai shi kuma sau 44 ana fadawa gwamnatin Buhari cewa za a kai hari gidan kurkukun Kuje dake babban birnin tarayya.

Saboda haka shi yana ganin kawai a dakatar da hawa baburan a wuraren da ake tunanin ya kamata amma gabadaya kasa ba.

Karanta wannan  Shugaba Ghana yace bai cewa Tinubu yaje ya nemi lafiya kuma ya janyewa Peter Obi ba

A makonnin da suka gabata ne ‘yan ta’addan ISWAP suka kai hari gidan kurkukun inda suka kashe jami’ai kuma suka sako masu laifi sama da 900, amma an kamo wasu yayin da wasu kuma suka koma da kansu.

Sai dai fa har yanzu akwai kusan 400 da ba a gansu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.