Friday, May 29
Shadow

Saudiyya ta gargaɗi limamai kar su gudanar da Sallar Idi’

Ma’aikatar harkokin addinin musulunci a Saudiyya ta gargadi limamai a ƙasar da kada su gudanar da Sallar Idi, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Ministan harkokin addinin musulunci, Sheik Abdullatif Al-Asheikh ne ya umarci yin hakan a wata sanarwa da ma’aikatarsa ta fitar.

Wannan wani yunƙuri ne na dakatar da taruwa a masallatai kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bada umarni domin daƙile yaduwar cutar korona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *