fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Saukata daga mulki ba zata sa matsalar tsaro ta warware ba>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, saukarsa daga mulki ba zata sa matsalar tsaro ta kwaranye ba.

 

Shugaban yace babu abinda zai sa ya sauka daga kan mulki inda yace wasu ne ke wa gwamnatinsa zagon kasa.

 

Shugaban ya kara da cewa masu kiran ya sauka dabara ce ta wasu dake son hawa mulkin Najeriya ko ta halin kaka.

 

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari tunda ya gaza samar da tsaro ya sauka daga mulkinsa.

Karanta wannan  Hotunan barayin waya da aka kama a Kano

 

Kuma wannan martani da alama shugaban da kungiyar yake.

 

A cikin kwanakinnan dai, hare-hare na kara munana a hanyoyin Najeriya inda ake ci gaba da sace mutane dan kudin fansa.

 

Ko a Safiyar yau, saida aka samu Rahotannin sace wasu dalibai mata a jihar Zamfara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.