fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Saurayi yayi garkuwa da budurwarsa saboda ta takura masa sai ya aureta

Wani mutum, Bello Ahmed dake zaune a Dubai ta kasar UAE yayi garkuwa da budurwarsa saboda ta takura masa ya aureta.

 

Bello dan shekaru 25 yace ya sace budurwarsa dan ya samu kudin da zai aureta.

 

Ya hada baki da wasu mutane, Ibrahim Mohammed, 30, Bilyamiyu Mohammed, 30, da Uche Daniel, 30.

 

Bello ya zo Najeriya dan yin wannan aika-aika, inda suka hada baki, yana zaune da budurwar tasa a daki wadda lauyace, sai ga abokan nasa sun shigo suka saceshi da budurwarsa dan kada ta gane.

Karanta wannan  SIYASA: Ya Kamata Matasa Ku San Ciwon Kanku Ku Daina Yarda 'Yan Siyasa Na Amfani Da Ku Suna Azurta Kawunansu

 

Saidai dan uwan budurwar dansanda ne wanda ya kai karar lamarin kuma aka fara bincike aka ganosu.

 

Bello dai nada mata da yara 2 a Dubai, yana son auren Hannah ne a matsayin matarsa ta 2.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.