fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Saurayin Da Muka Hadu A Facebook Yayi Yunkurin Samini Guba A Abinsha Na

Daga Tonga Abdul Tonga

Wata budurwa ta bada labarin yadda wani wanda take abota da shi a shafinta na Facebook ya gayyaceta, inda yaso saka mata guba a abinsha daya kawo mata.
“Abokina nane a shafina na Facebook. Duk abunda zan yi posting sai yayi mini koment. Hakan yasa muka saba dashi tamkar munsan juna. Sai ya gayyaceni bukin ranar zagayowar haihuwarsa”. Injita.

Tace duk kokarin da yayi ta amsa gayyatar nasa taki. Ganin bata hakarta gayyatan mutumin da batasan shi.

“Duk da ina son haduwa dashi, saboda mutun ne mai basira wajen yin sharhi. Amma dai naki amincewa da gayyatarsa sai ana sauran kwana guda bukin ya nace nace masa zanzo.

” Bayan na isa gidan abincin da za ayi bukin kamin ma na shiga ciki sai na hango shi a tsaye a kofar mota daya fito wani ke tukashi. Ban wahala wajen ganeshi ba saboda hoton daya saka a shafin nasa. Bayan ya tarbeni mun shiga ciki ne sai na lura ni kadai ce da shi ba buki bane kamar yadda nayi tsammanin fati ya shirya ya gayyaci mutane “. A cewarta.

Inda ta ci gaba da cewa, ” yayi juyin duniyan nan a kawo mini abinci naci nace a koshe nake. Kuma tabbas a koshen nake. Daga karshe ya sa aka kawo mini lemun kwalba. Bayan bude lemun ne har na soma sha sai aka nemi yazo ya karbi bil na kudin daya ci, inda ya bukaci na karbo masa. Ina dawowa sai na fahimci an taba kwalban dana bari ba a yadda na barshi yake ba. Dana kula sai na fahimci yana kumfa kamar yadda aka bude ko aka girgiza. Ganin hakan sai bance komai ba. Bayan wasu yan mintuna da zama na ne nace masa zan wuce. Nan fa ya nace sai na shanye lemun nan, nace masa ya isheni amma sam yaki. Daga karshe nace masa zan wuce da shi gida zan sha a can. Na mike zan tafi.

Karanta wannan  Hotuna: Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta shiga ofishinta na uwargidan shugaban kasa a karon farko

“Ya bukaci nazo su saukeni amma kamin nayi magana sai ga wani mai adaidaita kamar nice daman yazo dauka, kawai sai nace masa ai ga mai daukata yazo. A haka mukayi sallama ya ciro kudi ban san ko nawa bane saboda sabbi ne ‘yan 100 naki karba ko tabasu banyi ba cikin fushi ya bar wajen nawa. A hanyar komawata ne na sake duba lemun nan sai naga kwayar daya saka mini ta narke sai wata ‘yar guntuwa bata gama jika ba na cire ta na daure. Bayan na koma gida ne na nunawa wani mai shagon sayar da magunguna yace mini magani mai bugarwa da kauda hankalin mutum nan take. Ya fadamini sunan maganin amma bazan ambata ba anan”.

‘Yan matan daga karshe ta ja hankalin ‘yan mata irinta dasu yi hankali da irin mutanen da suke haduwa dasu a shafukan sada zumun

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *