Kungiyar kare hakkin bil’adama ta SEFAP ta sake maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu kan kulle kafar sada zumuntar Twitter.
A yau kotun ECOWAS ta gargadi gwamnatin Najeriya cewa kar ta sake maimaita kuskuren data yi na kulle kafar sada zumuntar domin ba daidai bane.
Wanda biyo bayan hakan itama kungiyar SERAP ta maka shugaban kasar a kotu cewa a umurce shi ya baiwa ‘yan kasa bakuri kan kulle kafar sada zumuntar daya yi.
A watan yuni na shekarar 2021 ne shugaban kasar Najeriya ta kulle kafar sada zumuntar zuwan watan janairu na shekarar 2022 kan goge maganar daya yi ta gargadi ga haramtacciyar kungiyar IPOB.