fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

SERAP zata maka shugaba Buhari a kotu kan kama wani dan jaridar daya tona asirin tsohon shugaban soji wato janar Burtai

Kungiyar dake kare hakkin bil’adama ta SERAP ta umuci shugaban kasar Najeriya cewa ya gaggauta bayar da umurni a saki dan jaridar Gazette da aka kama yau ranar juma’a.

Hukumar ‘yan san ta kama John Adenekan a yau ranar 22 ga watan Yuli a ofishin ‘yan jarida na Peoples Gazette dake babban birnin tarayya kan tona asirin daya yi na kudin makamai da janar Burtai ya sace.

Kuma bayan sun kama shi hukumar ta dawo ta sake kama wasu ma’aikatan gidan jaridar guda hudu duk dai a yau ranar juma’a.

Karanta wannan  Najeriya zata iya lalacewa idan kuka cigaba da sukar mulkina, cewar shugaba Buhari

Wanda hakan yada kungiyar dake kare hakkin bil’adama ta SERAP ta umurci shugaba Buhari ya gaggauta bayar da umurni a sako su ko kuma su maka shi a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.