fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Sergio Ramos ya samu rauni yayin da Cadiz ta lallasa Real Madrid 1-0 a gidan ta

Zidane da tawagar sa sun sha kashi a gidan su a hannun kungiyar Cadiz wadda tayi nasarar cin kwallo guda a wasan tun kafin kafin aje hutun rabin lokaci, yayin da kuma wasan ya kasance karo na farko da kungiyar tayi nasarar cin wasa tsakanin tada Real Madrid a tarihin ta na shekaru 110.

Kaftin din Real Madrid Segio Ramos ya samu rauni a gwiwar kafar shi ta hagu tun kafin aje hutun rabun lokaci kuma har aka dawo daga hutun bai dawo wasan ba wanda hakan yasa aka maye gurbin shi da Eder Miltiao. Real Madrid zata buga wasan Champions League da kungiyar Donetsk a gidan ta ranar laraba kuma zata ziyarci Barcelona ranar sati mai zuwa a gasar La Liga.
Saboda haka da yiyuwar Sergio Ramos ya rasa wa’yan nan wasannin idan har raunin nshi mai tsanani ne yayin da kuma ya zamo dan wasan na 14 daya samu rauni a kungiyar kama daga shirye shiryen sabon kaka har izuwa yanzu da aka fara buga kakar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *