fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Shafukan Facebook da WhatsApp da Instagram sun daina aiki a yammacin Juma’a

Shafukan Facebook da Instagram da WhatsApp sun daina aiki a sassa da dama na duniya a yammacin Juma’a abin da ya tunzura da dama daga cikin masu amfani da shafukan.

Shafukan na sada zumunta mallakar mai kamfanin Facebook, da Messenger tun daga karfe 5:30 agogon GMT suka tsaya.

Masu amfani da shafin idan suka yi ƙoƙarin buɗe wa suna cin karo da irin wannan sako da ke cewa ‘5xx Server Error’, wato alamar matsala ba tare da wani cikakken bayani ba.

Hakazalika da dama daga cikin masu amfanin da shafin Facebook sun ce sun gaggara iya shiga shafin, koda yake kashi 63 cikin 100 na masu amfani da shi ne suka ce an datse su baki ɗaya.

Mutane dai sun yi ta bayyana takaicinsu da ƙorafi a shafukan sada zumunta kan gaggara iya tuntuɓar abokansu da iyalai ko abokan aiki na wani lokaci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.