Saturday, April 4
Shadow

Shahrarran tauraron fina finan Kannywood Ali Nuhu ya musanta jita jitar da ake yadawa akan ya kamu da cutar Covid-19

Shahrarran tauraron fina finan Kannywood Ali Nuhu ya musanta jita jitar da ake yadawa akan ya kamu da cutar Numfashi wadda aka sani da Covid-19.

Jarumin na cikin sahun Jaruman masana’antar kudanci Najeriya Nollywood wanda suka ziyarci bikin bada kyautar girma na (AMVCA) da ya gudana a Jihar lagos.

An rawaito cewa Ali Nuhu shida wasu yan Kannywood su hudu suka ziyarci bikin a ranar asabar 14 ga watan Maris 2020.

Wanda biyo bayan bikin keda wuya sai gwamnatin legas ta umarci duk wanda ya hallaci wajan ya tabbata an gwada shi sabuda an samu wanda ke dauke da cutar wanda ya hallaci bikin.

Nuhu ya bayyana cewa yau kimanin satin sa biyu da halattar taron wanda a cewar sa hakan ya nuna bashi da wata matsala sakamakon cutar bata daukan lokaci kamar haka, ya kuma kara da cewa akwai jarumai dadama wanda sun hallaci taron amma babu wanda ya ji ya samu wata matsala.

Sai dai kuma a wani rahotan ya nuna an samu mutuwar wani jarumi mai suna Alkali Matt, wanda aka rawaito ya halacci bikin bada kyautar girma da ta gudana a lagos, (AMVCA) inda ake rade radin yayi hulda da mai dauke da cutar Covid-19 .

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *