Shalelen Paris Sainte Germain, Kylian Mbappe ya samu sabani da Messi kan sayar da Neymar a wannan kakar, cewar Mundo Deportivo.
Mbappe ya bukaci kungiyar ta sayar dashi amma shi kuwa Messi bai goyi bayan a sayar masa da abokin wasan nasa ba.
Mbappe yanzu yanada karfi sosai a PSG duba da ya sabunta kwantirakinsa izuwa shekarar 2025 a kungiyar yayi burus da Madrid.
Amma da yiyuwar Neymar ya cigaba da wasa a PSG saboda kwantirakinsa sai 2027 zai kare kuma farashinsa zaiyu ysada sosai.