An kama wani mutum a jihar Legas, James Olajoyetan da shekaru 67 da ake zargi da yiwa wata yarinya ‘yar shekaru 12 fyade.
Mutumin an zargeshi da yiwa yatinyar Fyade sau 4 tun bayan da ta je Legas din yin bikin sallah a wajan kakanta wanda Makaho ne. An zargeshi da fara yiwa yarinyar fyade a dakin kakan nata.
Ranar da dubunsa zata cika, ya kira yarinyar ne da ya aiketa inda taje ta tsaya a bakin kofa amma yace ta shiga dan ya bata kudin, yarinyar tace tana shiga sai ya garkame kofa ya fara lalata da ita. Makwabta sun ji kuka inda daga nanne suka balla kofar dakin suka kamashi turmi da tabarya da yarinyar.
An mukashi hannun ‘yansanda saidai yace karya aka masa sau 1 ne yayi lalata da yarinyar kuma shima yana tunanin wani fastone ya tsine masa shiyasa ya aikata hakan.