fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Sharri ake min, ban saci dukiyar gwamnati ba>>Janar Buratai

Tsohon shugaban sojojin Najeriya,  Janar Tukur Yusuf Buratai ya musanta zargin da ake masa na satar dukiyar gwamnati da kuma mallakawa kansa wasu kadarorin gwamnatin.

 

Lauyan Buratai, Osuagwu Ugochukwu ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja inda yace kotun da’ar ma’aikata ta binciki Buratai kuma ta wankeshi daga zargin da ake masa.

 

 

Yace maganar mallakar kadarori a Najeriya da Dubai, maganace wadda kusan shekaru 6 da suka gabata aka kammala ta, dan haka kawai yamadidi ne ake so a yi da sunan Buratai.

Karanta wannan  Gwamnatin jihar Ondo zata baiwa duk wanda ya kawo mata labaran sirri na 'yan bindiga naira dubu hamsin

 

Dan hakane ya nemi wanda suka yada wancan labari da su janyeshi ko kuma au fuskanci hukunci ta hanyar shari’a.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.