SHAWARA CE๐๐ฝ
Don Allah kada a hada kai da kai a zalunci wani.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Ka yi aikin kirki, domin duniya ba matabbata ba ce.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Ka tsaya a kan gaskiya, duk rintsi duk wahala.
SHAWARA CE๐๐ฝ
In ka ga wasu suna husuma, yi iya bakin qoqarinka ka sasanta, sai dai in abin ya fi qarfinka.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Ka guji hassada, domin bayan haddasa gaba dazatayi tsakanin ka da dan’uwanka, zata kuma cinye ayyukan ka.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Ka rike girmanka da Allah ya ba ka, domin ba dabaranka ne yakawo maka girman ba.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Kadauki na sama dakai a matsayin iyayenka, sa’anninka a matsayin abokanka, na kasa dakai a matsayin ‘ya’yanka.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Shiga haqqin mutane ba shi dakyau, Allaah ne Ya hana, ka guji yin hakan, domin zai kaika ga halaka.
SHAWARA CE๐๐ฝ
Kada kayi don ka faranta ko munana wa wani, kada kuma kayi dan wani, domin ba shine ya halicce ka ba .
Allah ya bamu ikon dauka