fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Sheffield 3-0 Chelsea:Sun fi mu karfi>>Lampard

Kwallayen McGoldrick guda biyu da kwallon McBurnie sun taimakawa Sheffield United a jiya yayin da suka ba Chelsea kashi har 3-0, bayan Chelsea sun yi nasara akan Palace da Watford.

Manajan Chelsea Frank Lampard ya bayyana cewa wasanni biyu da aka cisu cikin wasanni hudu da suka gabata babban sako ne ga tawagar tashi wanda watakila zasu iya tsintar kansu ana biyar idan har United suka yi nasara a wasan su da Southampton.

Bayan an tashi wasan Lampard yace Sheffield United sun fi su a zahirance, sun fi su yin kokari a wasan, kuma sun fisu yin wasa da kwallon. A karshe ma yace sun fisu karfi. Kuma shi maganar Sheffield United kawai yake ji yayin da suke buga wasan.

Karanta wannan  Manchester United ta ragewa Ronaldo albashi bayan yace zai sauya sheka a wannan kakar

Ya kara da cewa watakila zasu tsinci kansu na biyar a saman teburin gasar amma duk da haka zasu cigaba da kokari domin su kasance cikin kungiyoyi hudu dake saman teburin gasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.