fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Shehu Sani yayi Allah wadai da harin da aka kaiwa tsohuwar makarantarsa, inda aka sace dalibai

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai wa tsohuwar makarantarsa, Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati (GSC) Kagara, a jihar Neja hari.
Sani a cikin wani sako a ranar Laraba ya ce shugaban makarantar ya fada masa cewa an sace wasu dalibai da malamai a safiyar ranar Laraba.
An tattaro cewa mutanen dauke da makamai sun afkawa makarantar ne cikin kakin soji.
Da yake mayar da martani, Shehu ya ce, “Da sanyin safiyar yau, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun afka wa Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara Jihar Neja, suka yi awon gaba da wasu dalibai da’ yan uwa ma’aikatan. Na yi magana da shugaban makarantar.
”Hotunan da bidiyo na wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Neja wadanda suka hada da mata, yara da jarirai, wannan tsantsan mugaci ne da ban tausayi. Karfin hali da ƙarfin gwiwa na yan fashi da makami suna nuna matsala babba da yakamata Gwamnati ta hanzarta yi domin ceton al’ummar kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *