Tsohon sanatan jihar kaduna, Shehu Sani ya yayi kira ga ‘yan siyasar dake shirin gudanar da yakin zabe a karamar hukumar Birnin Gwari dake Kaduna.
Inda yace su kula domin akwai wata kungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru data hana gudanar da kamfe a yankin saboda haka su kula.
Jihar Kaduna na daya daga cikin johohin arewacin Najeriya dake fama da tsaro a kwanankin nan, yayin da a makon daya gabata aka kai hari coci aka kashe mutane kuma aka yi garkuwa da wasu.