fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana sirrin haddar Alkur’ani

A hirar da aka yi da Shehin Malamin Addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayana sirrin Haddar Alkur’ani.

 

Yace ana samun yara masu shekaru 7 wasu ma da shekaru 5 suna haddace Alkur’ani.

 

Ga hirar da BBCHausa ta yi dashi Kamar haka:

 

Gaskiya ne da farko muna da asiri na Alkurani da iyayenmu suka samu a Borno wajen Bare-Bari, da shi muke amfani wajen haddar Alkur’ani.

“Daga bisani lokacin da Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana ya ce ya roki Allah ya ba shi karamar haddar Alkur’ani, sai ya zama shi kenan an huta da nemo maganin karatun Alkur’ani Shehu ya riga ya roki Allah mutane su haddace Alkurani cikin sauki,” in ji shi.

”Za ka samu yaro mai shekara bakwai ya hadadce Alkur’ani, har mai shekara biyar ma ya haddace Alkur’ani,” in ji malamin.

”Na gode wa Allah, babban abin da Allah ya ba ni babu kamar Musulunci da son Annabi Muhammdu (S.A.W), da haddace Alkur’ani, ya kuma kara min da karbar darikar Sheik Tijjani jikan Manzon Allah.”

Malamin ya ce ya tattaba karatuttuka amma wanda yake da shaida a kai shi ne haddar Alkur’ani, da tafsiri wanda ya ce su kan su manyan malaman tafsirin sun tabbatar ya iya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Labari me dadi: Gobe zamu janye yajin aiki, cewar ASUU

Leave a Reply

Your email address will not be published.