fbpx
Monday, August 3
Shadow

Shekara Guda Da Batan Dadiyata

Shekara guda kenan bayan ‘batan Abu Hanifa Dadiya. Ranar 1 ga watan August 2019 wasu suka je unguwan Barnawa har gidan shi suka dauke shi. Yau kimanin shekara guda daidai kenan babu wani kamshin labari game da shi. Wannan babban kalubale ne ga jami’an tsaro, an kuma take masa hakki, sannan kuna cutarwa da kuma iyalan sa.

 

Kafin batan shi Abu Hanifa, marubuci ne a shafukan sada zumunta kuma yana rubutu a tsarin tsawon rai da kwalliya wato ‘blogging’ shi de ‘blogger’ dan akidar ‘Kwankwasiyya a siyasa, ya yi shura a wannan fannin. Da shi da abokan shi da suke irin wannan aikin sun sa fuskantar barazana daga hukumomin tsaron DSS wasu ma an kama su an sake daga baya.

An yi ta kiraye-kirayen sakin shi daga ‘kungiyoyin kare hakkin bil adama da wasu daban, an yi ta tarukan manema labarai game da rubuce-rubuce da tarukan salloli da addu’o’i kan haka amma babu wani abinda ya canza.

 

Abu Hanifa, ya bata ya bar matar sa, ‘yarsa sannan yana da mahaifiya. Mabiya akidar Kwankisiyya da wasu daga jam’iyar PDP suna ganin sakacin jami’an tsaro da Gwamnatin jihar Kano wajen ganin an samo shi.

 

Ko wane mataki hukumomi za su dauka nan gaba game da hakan bayan ya cika shekara guda babu labarinsa?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *