Wani shirin gidan talabijin na kasar Andulus/Sfaniya ya ruwaito cewa tauraron dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo zai bar kungiyar Real Madrid a shekara me zuwa idan Allah ya kaimu, dan shekaru 32, Ronaldo ya riga ya sanar da shugaban Real Madrid din, Florentino Perez cewa zai bar kungiyar shekara me zuwa, kamar yanda rahoton ya bayyana.
Amma rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta Real Madrid bata son tafiyar dan wasan nata, duk da yake cewa Ronaldon yaki sabunta kwantirakinshi na tsaya a kungiyar.
Haka kuma an ruwaito cewa Ronaldon baiji dadin rashin nasarar sayan Kylian Mbappe na kungiyar Monaco da kungiyar tashi tayi ba, wanda PSG ta kasata.
Da kafar watsa labarai ta Bein Sport take mai tambaya a farkon watannan akan ko zai sake rattaba hannu dan sabunta Kwantirakinshi a Real Madrid din? Ya bayyana cewa “bazan sabunta ba, bazan sabunta ba”
“Kwantirakin da nike dashi yanzu ya isheni”
Ronaldo shine dan wasan da yafi ciwa Kunguyar Real Madrid din kwallaye a tarihi, inda a wasanni dari hudu da bakwai daya buga, yaci kwallaye dari hudu da sha hudu, tun bayan da yazo daga Manchester United a shekarar 2009 akan kudi fam miliyan tamanin.
Haka kuma ya taimakawa Real Madrid din daga kofina goma sha uku, ciki hadda kofin zakarun turai guda uku da kuma kofin Laliga guda biyu.
A farkon makonnan ne aka haifawa Cristiano Ronaldon diya mace da yakai yanzu ‘ya’yanshi hudu kenan .