fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Shekau yawa Shugaban kasar Chadi Barazana a sabon Bidiyo

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya mayar da martani ta sautin murya kan harin da kasar Chadi ta kaiwa mayakansa.

 

Sakon me tsawon mintuna 5 da jaridar Thenation ta samu an ji Shekau na fadin cewa Idris Derby na cikin matsala tunda ya taba Allah.

 

A cikin Sakon Shekau yace kisan da sukawa sojojin Chadi Allah ne ya basu nasara kuma duk abinda Idris Derby din zai musu to ba zai yi Nasara a kansu ba.

 

Shekau yayi kira ga mayakanshi da kasa du gudu su jajirce dan irin wannan abu ya faru a baya kuma tunda suna tare da Allah to zasu yi Nasara.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada Aliko Dangote a matsayin shugaban sabuwar kungiyar da zata kawo karshen cutar Malaria a Najeriya

 

Ya kuma yi kira ga jama’ar kasar Chadi da su tashi tsaye domin irin rayuwar da suke ba bisa shari’a take ba, yace idan kuma sun kiya to Allah zai basu Nasara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.