Cin Fuska Ne Ga Musulunci Barin Osinbajo Ya Shiga Masallaci Da Takalmi A Kano
DAGA Yasir Ramadan Gwale
Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Obama shi kansa da zai shiga Masallaci sai da ya cire takalmi watakila saboda ya girmama Musulmi da suke Sallah a ciki saboda ya san suna cirewa in za su shiga, amma shi Osinbajo ba wanda ya iya ce masa ya tube takalmi Musulmi ba sa Sallah da takalmi akan dadduma, gaskiya cin fuska ne ana kallonsa da takalmi amma ba wanda ya nuna masa ya cire alhali duk ‘yan tawagar kowa ya cire nasa da zai shiga.
Abin tambaya anan Masallacin Villa da Shugaban kasa idan zai shiga sai ya cire takalmi, haka idan Osinbajo zai shiga da takalminsa? Ai shikenan.
