fbpx
Friday, March 31
Shadow

Shima dai Gwamna Cross-River ya bada damar bude Coci-coci da Masallatai a ci gaba da Ibada

Alummar musulmin Kuros Riba sun cimma matsaya tsakanin su da gwamnatin jihar a kan yadda za su ci gaba da gudanar da addininsu kamar yadda aka saba.

 

 

Hakan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin Alhaji Tanimu Hassan, mataimaki na musamman a kan addinin Musulunci ga gwamnan jihar Farfesa Ben Ayade, da mataimakin gwamnan jihar Farfesa Ivara Esu, ganin cewa a karshen wannan mako ake sa rai a yi Karamar Sallah.

 

Alhaji Hasan ya shaida wa Aminiya cewa, “Mun tattauna da mataimakin gwamna yanzu, mu Musulmi za mu ci gaba da yin salloli a masallatai kamar yadda aka saba”.

 

Mataimaki na musamman kan addinin Musulunci ga gwamnan ya ci gaba da cewa “ko wanne masallaci kada ya haura mutum dari biyar.

Karanta wannan  Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya kafa Kwamitin karɓar mulki daga Gwamna Ganduje 

 

 

“Kuma kowa zai sa takunkumin rufe fuska, a ajiye ruwa da kayan wanke hannuwa a waje”.

 

Da aka tambaye shi game da Sallar Idi da ta Juma’a sai ya ce, “an bar mu mu yi Sallar Idi amma dokar bari a yi Sallar Juma’a za ta fara aiki daga 24 ga watan nan”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *