fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Shin Bidiyon da aka rika yadawa cewa an ji kiran sallah a dakin ka’aba gaskiyane?

Wani bidiyo da aka dinga yaɗawa a shafukan zumunta ya yi iƙirarin cewa an ji kiran sallah da kuma karatun Al-Ƙur’ani mai tsarki a ɗakin Ka’aba amma da aka duba ba a ga kowa ba.

Kazalika, wasu daga cikin masu yaɗa bidiyon da ke nuna mutane sun carko-carko a bakin ɗakin na Ka’aba, sun ce lamarin ya faru ne yayin da ake tsaka da ɗawafi a Masallacin Harami na Makkah.

Akasarin waɗanda suka yaɗa bidiyon ba su iya faɗar rana da lokacin da lamarin ya faru ba, waɗanda kuma suka faɗa sukan ce “a yau”, duk da cewa sun wallafa su ne a ranaku daban-daban.

A wannan makon ne aka dinga yaɗa bidiyon musmaman a Facebook da WhatsApp, akasari daga 17 ga watan Mayu.

A cikin bidiyon, an ga cincirundon mutane kusan kowa ɗauke da wayar salula na ɗaukar bidiyon ɗakin Ka’aba da aka ce babu kowa a ciki, inda ake jin muryar wata mata na yin addu’o’i da wani harshe muryarta na rawa kamar za ta yi kuka.

Shi ma wani Mohammed Babangida a Facebook ya wallafa bidiyon wanda mutum 63 suka kalla ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Irin dai wannan bidiyon da Imam Olayiwola ya saka a nasa shafin, an kalle shi sau 586.

Bincike ya nuna cewa iƙirarin da mutane suka dinga yi game da bidiyon babu gaskiya a cikinsa kwatakwata.

Kafar yaɗa labarai ta Haramain Sharifain mai kula da ayyukan ibada a Masallatan Harami na Makkah da Madina ya ce an ɗauki bidiyon ne a cikin watan Azumin Ramadan da ya gabata.

Ya ƙara da cewa an ɗauke shi ne a lokacin da jami’an tsaron masallacin ke yunƙurin shigar da wata tawagar ‘yan siyasa cikin ɗakin na Ka’aba yayin da ake gudanar da sallar Tahajjud, wato sallar tsakar dare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.