Rahotanni na yawo a kafafen sada zumunta cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zabi gwamna Zulum a matsayin abokin takararsa.
Masu hannu da tsaki a jam’iyyar ta APC sun bukaci a baiwa gwamnan jihar Boro Babagana Umara Zulum matsayin abokin takarar Tinubu.
Amma a halin yanzu dai Tinubu bai tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa ba.
Duk da cewa yana daya daga cikin manyan mutanen da Tinubu ke shirin zab a matsayin abokin takarar nasa.